Da yake tabbatar da hakan a birnin Yolan jihar Adamawa, babban hafsan sojojin saman kasar Air Mashal Sadik Abubakar, ya ce sojojin kasar ba za su yi kasa a gwiwa ba, wajen murkushe masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa. Sadik ya kara da cewa sojojin ba za su dakata ba, har sai sun tabbatar da kare dukkanin yankunan kasar daga ayyukan bata gari.
Tun daga watan Fabarairun da ya gabata ne dai sabon gungun tsagerun yankin na Niger Delta da aka fi sani da 'Niger Delta Avengers", suka fara matsa kaimi wajen kaddamar da hare hare kan kayayyakin kamfanonin hakar danyen mai da iskar gas a wannan yanki. Sun kuma sha ikirarin lalata kayayyakin kamfanonin dake aikin hakar danyen man, suna masu ayyana bukatar neman 'yancin yankin na Niger Delta.
Rahotanni sun tabbatar da cewa hare haren da maharan ke kaddamarwa a baya bayan nan, sun jawo koma baya game da yawan danyen man da Najeriyar ke fitarwa zuwa ketare, ya zuwa ganga miliyan daya da dubu dari hudu a ko wace rana, adadin da ya yi kasa matuka da abun da kasar ke hakowa a baya.(Saminu Alhassan)