Shugaban kungiyar kamfanonin kere-kere reshen kudancin tarayyar Najeriya Azubuike Okafor, ya bayyana karuwar hare-haren da tsagerun Niger Delta ke kaiwa kayayyakin kamfanonin hakar mai, a matsayin dalilin koma-bayan da ake fuskanta wajen samar da makamashi a kasar.
Mr. Okafor ya ce, duk da irin kokarin da gwamnatin kasar ke yi na ganin ta magance matsalar karancin wutar lantarki a sassan kasar, matakan barnata kayayyakin kamfanonin hakar mai na zama tarnaki ga kwazon mahukuntan kasar. Ya ce, hakan ya sanya masana'antu da dama dakatar da ayyukansu.
Mr. Okafor na ganin hanya daya da ta dace a bi domin warware wannan matsala, ita ce hawa teburin shawarwari da tsagerun na Niger Delta Avengers.
Wannan sabuwar kungiya ta tsagerun Niger Delta dai ta fara kaddamar da hare-hare kan kayayyakin kamfanonin hakar mai ne tun farkon watan Febrairun bana, inda 'ya'yanta ke bukatar samun cikakken 'yancin yankin na Niger Delta mai arzikin mai.
Tuni dai ayyukan kungiyar ya haifar wa Najeriya koma-baya a fannin yawan danyen mai da kasar ke hakowa, inda a yanzu aka koma hako man da bai wuce ganga miliyan 1.4 a ko wace rana ba.(Saminu Alhassan)