Shugaban Najeriya ya dauki hutun binciken lafiya sakamakon ciwon kunne a birnin London
Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya bar Abujan Najeriya zuwa birnin London na Burtaniya a ranar Litinin, domin neman maganin ciwon kunnen dake yake fama da shi, a cewar wata sanarwar fadar shugaban kasa.
Shugaba Buhari ya dauki hutun binciken lafiya na kwanaki goma domin kai ziyara a birnin London, inda zai samu ganin wani kwararren likitan kunne, hanci da kuma makoshi domin wani binciken lafiya, in ji wannan sanarwa. (Maman Ada)