in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 40,000 da rikicin Boko Haram ya yaba da gidajensu na zaune a kan iyakar Nijer
2016-06-14 10:26:16 cri

A jiya Litinin MDD ta ce, ta yi kiyasin mutane dubu 40 ne da rikicin Boko Haram na baya-bayan nan ya raba su da gidajensu ke zaune a garin Bosso dake kan iyakokin kasashen Najeriya da Nijer tun a ranar 3 ga watan Yunin wannan shekara.

Ofishin MDD mai kula da ayyukan jin kai ya tabbatar da cewar, akwai rashin kyaun yanayin tsaro a yankin na Bosso a sakamakon kazamin harin da aka kai a yankin. Mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric shi ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

Tun a ranar 7 ga watan Yuni, hukumomi da kungiyoyin ba da agaji suke ci gaba da yin nazari game da irin kayayyakin tallafin da ake bukata a yankin da nufin shigar da kayan tallafi zuwa yankunan. Mai magana da yawun MDD ya ce, ya zuwa yanzu, hukumomin agajin sun samu nasarar shigar da tallafin ruwan sha da biscuit da motar daukar marasa lafiya.

Sai dai kawo yanzu kashi 25 ne kadai aka samu na kudaden da ake bukatar don gudanar da aikin jin kai a yankin Diffa daga cikin dala miliyan 74 da ake bukata, kuma tuni aka fara amfani da kudaden domin samar da kayayyakin da ake da matukar bukatarsu. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China