in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faransa da Amurka sun kai farmaki ta sama kan sansanin IS dake Iraki
2016-05-03 10:30:41 cri

Daga watan Janairu zuwa wannan lokaci kungiyar IS ta kai hare-haren boma-bomai sau da dama a wurare daban daban na kasar Iraki, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar darurruwan mutane. Tashar internet ta ma'aikatar tsaron kasar Faransa ta ba da labari jiya Litinin cewa, sojojin kasashen Faransa da Amurka sun kai farmaki ta sama kan sansanin kungiyar IS dake kasar Iraki cikin hadin gwiwa

Rahotanni na cewa, kasashen biyu sun kai farmakin ne kan wata masana'antar kera boma-boman da kungiyar ke amfani da su wajen kai harin kunar bakin wake a birnin Qaim na kasar Iraki.

Bangaren 'yan sandan kasar Iraki ya bayyana jiya Litinin cewa, an kai harin kunar bakin wake da boma-boman da aka dasa cikin mota a wannan rana da yamma a yankin kudancin birnin Bagadaza, babban birnin kasar Iraki, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 16, a yayin da mutane 43 suka ji rauni. 'Yan sanda suna ganin cewa, watakila dakarun kungiyar IS ne suka kai wannan farmaki.

Wannan farmaki shi ne na biyu da aka kai kan musulmai mabiya darikar Shia a cikin mako guda a birnin Bagadaza. A ranar 30 ga watan Afrilu ma, dakarun kungiyar IS sun kai farmaki da boma-boman da aka dasa cikin mota a kudancin birnin Bagadaza, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 24, a yayin da mutane 38 suka jikkata.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China