in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar IS ta kai hari ga rundunar sojan kare gwamnatin Libya
2016-06-13 10:56:11 cri
Jiya Lahadi 12 ga wata, kakakin rundunar sojan kare gwamnatin hadin gwiwar al'ummomin kasar Libya ya gaskata cewa, a wannan rana, kungiyar IS ta kai harin kunar bakin wake har sau uku ga rundunar sojan a birnin Sirte dake yammacin kasar, amma bai sanar da adadin mutanen da suka rasu sakamakon wadannan hare-haren ba.

Cikin 'yan shekarun nan, kungiyoyin ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi suna kara habaka a kasar Libya saboda yanayin tashe-tashen hankula da kasar ke fuskanta. Shi ya sa, tun a watan Mayu na shekarar bana, rundunar sojan kare gwamnatin hadin gwiwar al'ummomin kasar ta Libya ta karfafa ayyukanta wajen yaki da kungiyar IS. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China