in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Liu Yandong: An sami sakamako mai kyau a shawarwari tsakanin manyan jami'an Sin da na Amurka a fannin ala'du
2016-06-07 20:54:44 cri
A yau Talata ne, mataimakiyar firaministan kasar Sin Liu Yandong da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry suka jagoranci babban taron shawarwari tsakanin manyan jami'an kasashen biyu a fannin al'adun karo na 7 a nan birnin Beijing.

A jawabinta, Liu Yandong ta ce ta gamsu da muhimmin sakamakon da aka samu a tsarin shawarwari tsakanin manyan jami'an kasashen Sin da na Amurka a fannin ala'du a cikin shekaru 6 da suka wuce.

Liu Yandong ta bayyana cewa, a shekarar 2010, bisa kokarin shugabannin kasashen biyu, an bullo da tsarin shawarwari tsakanin manyan jami'an Sin da na Amurka a fannin ala'du, tare da kyautata shi a kai a kai. Yanzu yanayin da ake ciki na yin mu'amala tsakanin kasashen biyu a fannin al'adu ya zarce abin da aka zata. Hakan ya bayyana mu'amala mai karfi tsakanin sassan biyu a wannan fanni.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China