in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Rasha sun lalata wani babban rumbun adana makamai na IS a Syria
2016-04-23 13:13:25 cri
Hukumar kiyaye tsaron kasa ta Rasha ta bayyana a ran 22 ga wata cewa, sojojin kasar Rasha sun latata wani babban rumbun adana makamai na kungiyar IS a kasar Syria, kuma bisa binciken da aka yi, an ce, mai iyuwa ne dakaru za su yi amfani da boma-bomai da bindigogi dake babban rumbun din domin kai hare-haren ta'addanci a lardin Homs da wasu yankunan kasar Syria, amma, a halin yanzu, sojojin Rasha sun lalata wannan babban rumbun adana makamai.

A wannan rana kuma, kungiyar IS ta fidda wata sanarwa cewa, kungiyar ta harbe wani jirgin saman sojan gwamnatin kasar Syria a yankin karkara dake gabashin babban birnin kasar, Damascus, sa'an nan kuma, kungiyar ta kama matukin jirgin. Amma ba a sami labari game da ikirarin kungiyar ba daga kafofin watsa labarai na gwamnatin Syria ba.

Haka kuma, cikin wata sanarwar da cibiyar hafsoshin sojojin kasar Amurka ta fidda, an ce, bisa binciken da kasar Amurka ta yi dangane da hare-haren sama da aka kai a kasar Syria da Iraq kwanan baya, an gano cewa, hare-haren saman da aka kai sun haddasa rasuwar fararen hula guda 20, yayin da 11 suka jikkata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China