A jiya Litinin, shugaba Omar al-Bashir na Sudan ya tarbi wakilin kasar Libya kana mai ba da shawara ga shugaban majalisar wakilan kasar Libya mai kula da harkokin Afirka Abdul-Moniem Yousif Busafita.
A jawabinsa ga manema labarai bayan ganawar tasu, Abdul-Moniem ya ce sun tattauna da shugaba al-Bashir game da yadda za su kara bunkasa huldar da ke tsakanin kasashen biyu, da yadda wannan dangantaka za ta amfani sassan biyu da jama'arsu, da kuma muhimmancin bunkasa tsaron kan iyakokin kasashen biyu ta hanyar kafa wata runduna.
Tun da farko dai kasar Libya ta zargi Sudan da mara baya ga 'yan tawayen Libya Dawan, wadanda ke fada da gwamnatin Libya wadda kasashen duniya suka amince da ita, batun da mahukuntan Sudan suka karyata.
A shekarar 2013 ne kasashen biyu suka tura dakarun hadin gwiwa don kare iyakokinsu daga bakin haure da ke shigowa kasashen ba tare da izni ba, yaki da 'yan ta'adda da yiwa motocin 'yan kasuwa rakiya da dai sauransu.
Sai dai a shekarar 2015 gwamnatin Libya ta yanke shawarar janye dakarunta daga rundunar hadin gwiwar. (Ibrahim)