Al-Koni ya bayyana a yayin da ya ke ganawa da jakadan Sin da ke kasar Libya Li Zhiguo a wannan rana cewa, Libya ta sake nanata cewa, za ta nuna goyon baya tare da tsayawa haikan game da batun tekun kudancin kasar Sin kamar yadda ya ke kunshe cikin sanarwar Doha, wadda aka fitar a yayin taron ministocin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da kasashen Larabawa karo na 7 da da aka yi a ranar 12 ga watan Mayu. Libya tana ganin cewa, ya kamata a bi ka'idar warware matsalolin yankunan kasa da ruwa ta hanyar shawarwari. Libya tana goyon bayan kasashen da batun tekun kudancin kasar Sin ya shafa da su martaba yarjejeniya, da daidaito da aka cimma tsakanin kasashen da ke wannan yanki, don yin shawarwari cikin aminci, ta hakan ne za a warware wadannan riginginmu cikin ruwan sanyi.
Haka kuma Al-Koni ya ce, an shiya taron ministoci karo na 7 na dandalin tattaunwar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa cikin nasara, lamarin da ya tsara alkiblar raya hadin gwiwar sada zumunta a sabon yanayin da muke ciki.(Bako)