in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi alkawarin samar da goyon baya ga gwamnatin hadin kan al'ummar Libya
2016-05-17 10:46:40 cri
An gudanar da taron ministocin harkokin waje kan batun Libya a birnin Vienna dake kasar Austria a jiya Litinin, inda aka gabatar da hadaddiyar sanarwa, wadda ta yi alkawarin samar da goyon baya ga gwamnatin hadin kan al'ummar kasar Libya.

Wakilai daga kasashe fiye da 20 ciki har da kasashe 5 dake na kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD da hukumomin kasa da kasa ne suka halarci taron. A cikin hadaddiyar sanarwar da aka bayar bayan taron, an ce, gwamnatin hadin kan al'ummar kasar Libya tana yunkurin gabatarwa MDD bukatar soke hana jigilar makamai don yaki da kungiyar IS da sauran kungiyoyin ta'addanci. Sanarwar ta ce, wannan yunkuri zai samu goyon baya.

Sanarwar ta bayyana cewa, gwamnatin hadin kan al'ummar kasar Libya ita ce gwamnati daya tak da za ta karbi gudummawar tsaro daga kasashen waje bisa doka, wadda take da ikon kare albarkatun kasar Libya. Don haka, wajibi ne babban bankin kasar da kamfanin samar da man fetur na kasar da sauran hukumomin tattalin arzikin kasar su kasance karkashin ikon gwamnatin hadin kan al'ummar kasar.

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry, ministan harkokin wajen kasar Italiya Paolo Gentiloni da firaministan gwamnatin hadin kan al'ummar kasar Libya Faizi Sarraj sun gudanar da taron manema labaru na hadin gwiwa bayan taron, inda Kerry ya bayyana cewa, kasa da kasa za su nuna goyon baya ga gwamnatin hadin kan al'ummar kasar Libya wajen sa kaimi ga MDD da ta soke hana jigilar makamai a cikin kasar, ko da yake bai kamata a tsaida kuduri cikin gaggawa ba.

Sarraj ya bayyana a gun taron manema labarun cewa, kasar Libya tana fatan kasashen waje za su taimaka mata wajen horar da sojojin kiyaye tsaro na kasar, maimakon tsoma baki a harkokin kasar ta hanyar aikin soja kai tsaye. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China