Essid ya bayyana cewa, kasar Tunisia za ta ci gaba da yin hadin gwiwar tabbatar da tsaro a yankin iyakar kasar ta da Libya, da daukar matakai ta hanyar hadin gwaiwa don tinkarar barazanar ta'addanci. Kana ya jaddada cewa, ya kamata kungiyoyi daban daban na kasar Libya su amince da gwamnatin hadin gwiwar al'ummar kasar da MDD ta riga ta amince, da mika iko gare ta.
Sarraj ya bayyana wa 'yan jaridun kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, manyan batutuwan da suka tattauna tare da Essid a yayin shawarwarin sun fi shafar yaki da ta'addanci, da tabbatar da tsaro da dai sauransu. Kana bangarorin biyu sun cimma daidaito game da mayar da saukar jiragen sama na kamfanin jiragen saman kasar Libya a filin jiragen sama na kasar Tunisiya.
A ranar 22 ga watan Maris na bana, kasar Tunisiya ta sake bude iyakar kasarta da Libya. Kafin hakan, an kaddamar da hari a birnin Ben Guerdane dake kudu maso gabashin kasar Tunisiya wanda ke kusa da iyakokin kasashen Tunisiya da Libya, hakan ne ya sa gwamnatin kasar Tunisiya ta rufe yankunan dake kan iyakar kasashen biyu. (Zainab)