Daya daga cikin masu aiki a cibiyar watsa labarai dake gadi ofishin shugaban kasar ta Libya Osama Badi ya shaida wa kamfanin dillancin labaru na kasar Sin Xinhua cewa, wani dan kunar bakin wake ne ya kaiwa masu gadin shugaban kasa a garin Bowerat Al-Hassan da ke kusa da Sirte hari, inda suka kashe masu gadin 18 kana suka jikkata 30, baya ga wasu masu gadin 4 da aka halaka gabanin kai harin bam din.
Wata majiya a babban asibitin Misrata ta tabbatar da cewa, an kai gawawwakin mutane 22, sannan tana jiran karin wasu gawawwakin.
Gwamnatin hada kai ta kasar Libya wadda ke samun goyon bayan MDD, ta kafa rukunin masu gadi a ofishin shugaban kasa ne a kokarin da ake na karya lagon mayakan IS. (Ibrahim)