in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gano gawawwaki a kalla 85 a gabar tekun Libya
2016-06-03 13:37:53 cri
A jiya Alhamis ne, kungiyar ba da agaji ta Red Cross a Libya ta tabbatar da cewa,ma'aikata sun gano gawawwaki a kalla 85 a gabar teku Zuwara da ke kasar ta Libya. Ana kyautata zaton cewa, wadannan gawawwaki na bakin haure ne da suka shiga kasar Italy ta barauniyar hanya bisa tekun Bahar Rum.

Wani ma'aikacin kungiyar Red Cross Possef ya fada wa wakilinmu cewa, a cikin wadanda suka mutu, akwai mata da yara, kuma ma'aikata masu aikin ceto na ci gaba da lalubo mamatan a bakin teku. Ya ce, hakan ba a tabbatar da dalilin mutuwar wadannan mutane ba.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China