in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya gabatar da ra'ayoyi biyar a kan batun tekun kudu
2015-11-22 17:42:48 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang a yayin da yake halartar taron kolin kasashen gabashin Asiya karo na 10 a yau Lahadi a birnin Kuala Lumpur na kasar Malaisiya, ya gabatar da wasu ra'ayoyi biyar a game da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a tekun kudancin kasar Sin.

Na farko shi ne, ya kamata kasa da kasa su yi alkawarin bin ka'idojin kundin tsarin MDD, su kiyaye zaman lafiya a duniya ciki har da yankin tekun kudancin kasar Sin.

Na biyu, ya kamata kasashen da abin ya shafa su yi alkawarin daidaita sabanin da ke tsakaninsu game da ikon mallakar kasa ta hanyar yin shawarwari bisa ga ka'idojin dokokin duniya.

Na uku, ya kamata Sin da kasashen ASEAN su yi alkawarin tabbatar da sanarwar matakan bangarori daban daban kan batun tekun kudu, a gaggauta yin shawarwari kan cimma ka'idojin matakan da za a dauka, don daukar matakai kan kyautata tsarin amincewa da juna da hadin gwiwa da juna a shiyyar.

Na hudu, kamata ya yi kasashen da ba sa cikin shiyyar su nuna girmamawa da goyon baya ga kasashen shiyyar kan kokarin da suke yi na kiyaye zaman lafiya a yankin tekun kudancin kasar Sin, su taka rawar da ta dace a maimakon su dauki matakan da za su iya tsananta halin da ake ciki a shiyyar.

Na karshe, ya kamata kasa da kasa su yi alkawarin kiyaye 'yancin zirga-zirgar jiragen ruwa da na jiragen sama a yankin.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China