Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Madam Hua Chunying ta tabbatar da hakan lokacin zantawa da manema labarai tana mai cewa tsarin kasar akan tekun kudancin ta a bayyanne yake kuma akan kari abinda ba za'a canza ba.
Madam Hua tana mai da martani ne dangane da rahotannin mujallar walla street Journal na kasar Amurka da ke cewa yadda kasar Sin ke harkokin raya tsibirin tekun bai hargitsa daidaito ba sai ma ya dawo da hakan. Ta tabbatar da cewar Sin zata cigaba da aiwatar da ayyukan zaman lafiya da daidaito a kan tekun na kudancin ta da sauran kasashen yankin kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN, za ta warware matsalolin da ake fuskanta ta hanyar tabbatar da tattaunawa da tuntuban juna, da kuma karfafa ka'idojin da tsarin yankin.