in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya sun nuna goyon baya ga matsayin kasar Sin game da batun ikon yankin tekun kudu
2014-12-08 11:05:55 cri
A ranar 7 ga wata ne, gwamnatin kasar Sin ta bayyana matsayinta game de karar da Philippines ta shigar kan batun ikon mulkin yankin tekun kudu, inda Sin ta jaddada kin amincewarta da karar, cewa kotun shiga tsakani ba ta da ikon sauraron korafin bisa dokokin da suka shafi dukkan fannoni. Kasashen duniya sun sa lura sosai kan wannan batu, kuma sun nuna goyon baya ga kasar Sin kan yadda take son warware matsalar yankin tekun kudu ta hanyar yin shawarwari.

Shugaban kwamitin harkokin wajen majalisar dokokin kasar Cambodia ya bayyana cewa, yana goyon bayan gwamnatin kasar Sin da ta warware matsala kan teku bisa ka'idar zaman lafiya a tsakanin bangarori biyu. Ya kamata Sin da Philippines su warware matsalar yankin tekun ta hanyar yin shawarwari kai tsaye, bai kamata sauran bangarori su tsoma baki cikin harkokin ba don magance tsananta matsalar.

Shugaban asusun kula da harkokin tekun kudu na kungiyar ASEAN na kasar Indonesia ya bayyana cewa, Sin da kasashen kungiyar ASEAN ciki har da kasar Philippines sun riga sun daddale sanarwa kan ayyukan bangarori daban daban da batun yankin tekun kudu ya shafa, inda suka yi alkawarin warware matsalar ta hanyar yin shawarwari, amma kasar Philippines ta yi gaban kanta wajen shigar da kara, wadda hakan ya sabawa alkawarin da ta yi.

A ganin wani masani dan kasar Myanmar mai suna U Tun, gwamnatin kasar Sin ta bayyana matsayinta a bayyane, kana tana tsayawa tsayin daka kan matsayin, kuma matsayin kungiyar ASEAN shi ne kasashen da abin ya shafa su warware matsalar da ke tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari cikin lumana. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China