in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kalla mutane 9 sun mutu yayin harin Boko Haram a Nijer
2016-06-02 20:46:32 cri

Jami'an tsaro a lardin Diffa da ke kudu maso gabashin jamhuriyar Nijar, sun tabbatar da mutuwar mutane a kalla 9 tare da wasu mutanen 13 da suka jikkata ciki hadda masu manyan raunuka, a wani hari da mayakan kungiyar Boko Haram suka kaddamar a garin Bosso.

Harin dai na jiya Laraba ya sanya dakarun sojojin gwamnatin kasar mayar da martani mai tsanani, inda suka samu nasarar harbe mayakan kungiyar har su 10.

A watan Febrairu na shekarar 2015 ne kasashen Najeriya, Kamaru, Nijar, Chadi da Benin, suka kafa wata rundunar hadin gwiwa mai sojoji 8700, a wani mataki na ganin bayan ayyukan mayakan na Boko Haram. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China