in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nijar na halartar taron shiyya kan yaki da Boko Haram a Najeriya
2016-05-15 13:33:42 cri
Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou na birnin Abujan Najeriya tun a ranar Jumma'a da yamma, inda yake halartar taron shiyya kan yaki da Boko Haram da aka bude a ranar Abasar da yamma, tare da takwarorinsa na Najeriya, Chadi, Kamaru da Benin, da kuma shugaban Faransa, Francois Hollande.

Taron ya biyo bayan wanda aka yi a birnin Paris shekaru biyu da suka gabata kan tsaron shiyya, kuma ya biyo bayan ganawar shugabannin kasashe mambobin kungiyar tafkin Chadi (CBLT) da Benin, da ya gudana a cikin watan Oktoban shekarar 2015 a birnin Niamey, wanda ya taimaka ga tantance shirin yaki da 'yan ta'adda a karkashin wata rundunar hadin gwiwa dake kunshe da sojoji dubu 8.

A yayin wannan haduwa ta Abuja, shugabannin kasashe biyar na shiyyar da shugaban Faransa zasu maida hankali musamman ma kan kimanta ayyukan da aka gudanar wajen yaki da kungiyar Boko Haram, a cewar wata majiya dake kusa da wannan batu.

Haka kuma za a tattauna bullo da wani shirin cigaba na bayan yakin domin kare mutane masu rauni da kuma taimakawa wadanda hare haren suka rutsa dasu samun lafiya da sake basu damar gudanar da rayuwarsu yadda ya kamata.

Idan ba a manta ba, rundunar Nijar ta shiga Najeriya, tun yau da watanni da dama, a cikin rundunar kawance tare da sauran rundunonin Chadi, Kamaru da Najeriya domin yaki da Boko Haram. Shigar ta Nijar a cikin yaki da Boko Haram ya biyo bayan musammun ma jerin hare haren kungiyar a yankunan Bosso da Diffa dake kuriyar gabashin Nijar mai iyaka da Najeriya, wadanda suka janyo mutuwar fararen hula dama da kuma sojoji.

Kungiyar Boko Haram dake kai hare harenta a arewacin Najeriya tun a shekarar 2009 da yankin tafkin Chadi tare kuma da kutsa kai a kasashen Nijar, Chadi da Kamaru, sun yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 20 da kuma janyo ficewar mutane fiye da miliyan 1.5 daga muhallinsu, a cewar wata majiyar tsaro.

Jihar Diffa dake fama da hare haren Boko Haram, na kunshe a halin yanzu da 'yan gudun hijirar Najeriya fiye da dubu 150, bayan kuma na cikin gida kusan dubu 20 da suka kaura daga gidanjensu, a cewar wata kididdigar hukumomin Nijar.

Nijar da Najeriya dai na raba kan iyaka gudu bisa tsawon kilomita 1500, inda kuma daga bangarorin biyu ake samun al'ummomin dake magana da harsuna guda musammun ma Hausa, Kanuri da Fulatanci. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China