Yarinyar, mai suna Amina Ali-Nkeki, na daga cikin wani gungun mutanen da aka ceto a yankin Baale, dake jihar Borno, in ji kakakin rundunar sojojin Najeriya, kanar Sani Usman, a cikin wata sanarwa, ba tare da bada wani karin haske kan ranar da aka kwato wadannan mutane ba.
'Yan mata 276 ne aka sace a makarantarsu ta sakandare dake Chibok a cikin watan Afrilun shekarar 2014, lamarin da kuma kungiyar Boko Haram ta dauki alhaki.
A kalla 'yan mata 57 suka samu nasarar tsira da kansu, amma kawo yanzu babu labarin sauran 'yan mata fiye da 200.
Kanar Usman ya bayyana cewa ayyukan da aka gudanar a ranar Talata a gandun dajin Sambisa a jihar Borno, sun taimaka wajen kawar da mayakan Boko Haram daga sansaninsu na Njimia da kuma ceto mutane 41 da suka yi garkuwa da su, yawancinsu mata da kananan yara ne.
Kuma babu wani sojan Najeriya da ya mutu a yayin wannan samame, in ji mista mista Usman.
Tawayen Boko Haram, da ya fara a shekarar 2009, ya salwantar da rayukan mutane fiye da dubu goma, musammun a arewa maso gabashin Najeriya.
Sojojin Najeriya sun samu babban ci gaba a yakin da suke da kungiyar Boko Haram a tsawon shekarar da ta gabata tare da samun nasarar karbe yawancin yankuna da a baya suke hannun Boko Haram. (Maman Ada)