in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD tana bukaci a ci gaba da yaki da Boko Haram
2016-05-14 13:15:25 cri
Jiya Jumma'a 13 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya fidda wata sanarwa ta shugaba, inda ya yi allah wadai da babbar murya kan harin ta'addanci da kungiyar Boko Haram ta kai a yankin tabkin Chadi, haka kuma, ya bukaci rundunonin sojoji na kasa da kasa da su ci gaba da yaki da Boko Haram yadda ya kamata.

Cikin sanarwar, kwamitin sulhu na MDD ya yi allah wadai da ayyukan kungiyar Boko Haram ta yi, kamar kashe fararen hula, janyo tashe-tashen hankula, shigar da yara sojoji da kuma lalata dukiyoyin fararen hula da dai sauransu. A sa'i daya kuma, kwamitin ya nuna yabo ga kasashen Kamaru, Chadi, Nijeriya, Nijer da sauransu, sabo da ci gaban da suka samu wajen yaki da kungiyar Boko Haram da kuma kwato yankuna daga hannun Boko Haram da dai sauransu, kaza lika, ya bukaci rundunonin sojoji na kasa da kasa dake wurin da su karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, yayin da suke inganta ayyukan sojan da abin ya shafa.

Bugu da kari, kwamitin sulhu na MDD ya nuna maraba sosai kan gudanar taron kolin tsaron yankin karo na biyu da za a yi a babban birnin kasar Nijeriya, Abuja a yau Asabar 14 ga wata, inda mahalarta taron za su tattauna kan tsarin yaki da kungiyar Boko Haram da wasu matakan da za a dauka da sauransu.

Haka kuma, sanarwar ta nuna cewa, hare-haren ta'addanci da wasu miyagun ayyuka da kungiyar Boko Haram ta aikata a yankin tabkin Chadi sun haddasa tabarbarewar yanayin jin kai mai tsanani a wannan yanki, 'yan kasar Nijeriya kimanin miliyan 2.2 ba su da wuraren zama a halin yanzu, kana, bisa kididdigar da aka yi, an ce, akwai 'yan gudun hijira sama da dubu 450 a kasashen Kamaru, Chadi da Nijer da dai sauran kasashen yankin a halin yanzu. Haka kuma, mutane kimanin miliyan 4.2 ba su iya samun isassun abinci a yankin tabkin Chadi. Don gane da wannan lamarin, kwamitin ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su ba da taimakon jin kai ga mutanen da abin ya shafa yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China