Dangane da wannan lamari, kakakin rundunar sojan kasar ya bayyana cewa, wasu mayakan Boko Haram sun kai hari ga wata tashar bincike ta soja dake garin Bosso na lardin Diffa, sa'an nan, sojojin kiyaye tsaron kasar sun mai da martani kan wadannan dakaru, inda suka hallaka mutane 10 daga cikinsu, sauran dakaru kuma suka gudu. A sa'i daya kuma, sojojin gwamnati guda uku sun jikkata.
Kaza lika, sojojin gwamnatin kasar Nijer suna ci gaba da neman sauran mayakan da suka kai hari da kuma suka tsere ta hanyoyin kasa da na sama.
Tun bayan kafuwarta a shekarar 2004, kungiyar Boko Haram ta janyo tashe-tashen hankula a yankin iyakar dake tsakanin kasar Nijeriya da Kamaru, haka kuma, bisa kididdigar da aka yi, an ce, tun shekarar 2009 ya zuwa yanzu, a kalla dakarun kungiyar sun kashe mutane dubu 15.
Haka kuma, a watan Fabrairu na shekarar 2015, kasashen Nijeriya, Kamaru, Nijer, Chadi da kuma Benin sun kafa wata rundunar soja mai kunshe da mutane 8700 cikin hadin gwiwa domin yaki da kungiyar Boko Haram. (Maryam)