in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Buhari: Najeriya ba ta kai ga murkushe Boko Haram cikin sauri ba dalilin cin hanci
2016-05-19 10:23:04 cri
Cin hanci na daya daga cikin dalilan kasawar rundunar sojojin Najeriya na murkushe Boko Haram cikin sauri, in ji shugaban Najeriya Mahammadu Buhari a ranar Laraba.

Fadawar yankunan Najeriya 14 hannun Boko Haram ya bata sunan rundunar sojojin Najeriya, in ji shugaba Buhari a yayin wata ganawa tare da babban Limamin Al-Azhar, Ahmed El-Tayeb, a Abuja, babban birnin Najeriya.

Sojojin Najeriya sun kusan lalata karfin yaki na Boko Haram bisa matakan da gwamnatinsa ta dauka domin kawar da cin hanci da kuma kyautata karfin sojojin kasar ta hanyar samar da kayayyaki, horo da kuma kyautata zaman rayuwar sojoji dake fagen daga, in ji shugaban Najeriya tare da kara cewa sojoji sun samu nasarar kwato dukkan yankunan dake hannun mayakan kungiyar Boko Haram.

Tare da yin maraba da tallafin musulmin duniya game da yakin da Najeriya take yi kan wannan bore, shugaban Najeriya ya bayyana cewa yaki da ta'addanci ya kasance wani yaki da rashin gaskiya, kuma ya zama wajibi addinin musulunci da ma sauran addinai su taimaka wajen wannan yaki.

Shugaba Buhari ya jaddada niyyar gwamnatin kasar na sake tsugunar da dukkan mutanen da suka kaura dalilin rikicin Boko Haram. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China