Ranar 1 ga wata, zaunannen wakilin kasar Faransa a MDD Francois Delattre, wanda ke shugabantar kwamitin sulhu na MDD a wannan wata ya ce, mambobin kwamitin za su tattauna kan kyautata injuna mallakar rundunar wanzar da kwanciyar hankali ta MDD a kasar Mali da kuma kwarewar sojojin rundunar ta gudanar da aikinsu a wannan wata.
Dangane da lamarin, madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana yau 2 ga wata a nan Beijing cewa, kasar Sin ta yi tir da harin ta'addanci da aka kai wa rundunar wanzar da kwanciyar hankali ta MDD a kasar Mali a ranar 31 ga watan jiya. Kasar Sin na mara wa kwamitin sulhu na MDD baya wajen yin tattaunawa kan yadda za a inganta aikin tsaro yayin da sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD suke gudanar da aikinsu. (Tasallah Yuan)