Baki daya rundunar sojan kiyaye zaman lafiya da Sin ta tura zuwa Mali karo na uku tana kunshe da membobi 395, wadanda suka hada da injiniyoyi, da jami'an tsaro, da kuma likitoci. Wa'adin aikinsu ya kai tsawon watanni 8. An raba su zuwa rukunoni biyu don zuwa kasar Mali. Manyan ayyukansu sun hada da tabbatar da tsaron ofishin kwamandan dake yankin gabas na tawagar MDD a Mali, da yin gyare gyare ga hanyoyi da gadoji da hanyoyin saukar jiragen sama da dakunan sojoji da sauransu, da ba da jiyya da jigilar sojoji masu kamuwa da cututtuka da sojoji masu jikkata da dai makamantansu.(Fatima)