Hua Chunying ta bayyana hakan ne a yau Laraba 1 ga watan Yuni, inda ta ce, an kaiwa tawagar jami'an wanzar da zaman lafiya hari a sansanin tawagar ta MDD dake kasar Mali, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane da dama, cikin har da sojan kasar Sin guda daya, yayin da sojojin Sin guda hudu suka jikkata.
A cewarta, wannan al'amari ya bata ran kasar Sin, kuma gwamnatin na nuna matukar juyayi, tare da jajantawa iyalan sojan na Sin da ya rasu, da kuma jajantawa 'yan uwan sojojin da suka jikkata.
Bugu da kari, Hua Chunying ta jaddada cewa, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen goyon bayan aikin kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa, za ta kuma ci gaba da goyon bayan aiki kiyaye zaman lafiya, da zaman karko a nahiyar Afirka. (Maryam)