Rukunin dai na kunshe da dakarun soji 395, wadanda suka hada da sojoji ma'aikata, da na masu tabbatar da tsaro da kuma reshen likitoci.
Ofishin kula da harkokin kiyaye zaman lafiya na ma'aikatar tsaron kasar Sin ya bayyana cewa, rukunin sojin na biyu, zai tashi zuwa kasar Mali ne cikin watan Satumba mai zuwa.
Kaza lika ofishin ya ce za a jibge sojojin ne a birnin Gao, inda za su gudanar da ayyukan ginin hanyoyi da gadoji, da gyara hanyoyin filayen jiragen sama, da gine-ginen sansanin soja, da tabbatar da tsaro a sansanin, da kuma aikin jinya ga marasa lafiya da dai sauransu. (Zainab)