Kwamitin sulhun MDD ya bukaci Mali ta yi bincike kan harin da aka kaiwa sojojin kiyaye zaman lafiya
Kwamitin sulhun MDD ya fidda wata sanarwa, wadda ke Allah wadai da harin da aka kaiwa sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD dake kasar Mali, tare da kalubalantar mahukuntan kasar da su gaggauta gudanar da bincike, domin damke wadanda suka kaddamar da harin.
A daren ranar 18 ga watan nan ne ofishin magatakardar M.D.D. ya bayyana cewa, an kai hari ga sojojin kiyaye zaman lafiya na M.D.D. da ke kasar Mali a yankin Kidal, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji 5, tare da jikkatar wasu 3. (Zainab)