in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin da aka kai kan ayarin motocin sojojin MINUSMA ya haddasa mutuwar mutane 5
2016-05-30 10:13:11 cri
An kai hari kan wani ayarin motoci na sojojin kiyaye zaman lafiya na M.D.D. da ke kasar Mali MINUSMA a birnin Sevare da ke yankin tsakiyar kasar Mali a jiya Lahadi, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 5, kana mutum guda ya ji rauni mai tsanani.

Shugaban tawagar MINUSMA Mahamat Saleh Annadif ya yi Allah-wadai da wannan lamari, inda ya bayyana cewa, harin ta'addanci da aka kai wa sojojin kiyaye zaman lafiya ya keta dokokin kasa da kasa da hakkin dan Adam.

Ranar 29 ga watan Mayu, rana ce da aka kebe a matsayin ranar ma'aikatan da ke aikin kiyaye zaman lafiya na duniya. Annadif ya ce, a daidai wannan lokaci, an kai harin ta'addanci kan sojojin kiyaye zaman lafiya, lamarin ya kazanta. Don haka ya yi kira ga bangarorin da abun ya shafi da su yi kokarin zakulo wadanda suka kai hare-haren kan sojojin Mali da ayarin motocin sojojin kiyaye zaman lafiya na M.D.D.

A ranar 27 ga wata ne, aka kaiwa motoci sojojin Mali guda 2 da ke tafiya a yankin arewacin kasar harin bam, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji 5, tare da jikkatar wasu 4.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China