Wata sanarwa da shugabar hukumar zartarwar kungiyar Nkosazana Dlamini Zuma ta rabawa manema labarai, ta yi Allah-wadai da hare-haren da aka sake kaiwa dakarun gwamnatin Malin a yankin Ansongo da kuma wanda aka kaiwa sojojin kasar Togo da ke aiki a tawagar MINUSMA a kasar ta Mali, hare-haren da suka haddasa mutuwar sojoji da dama kana wasu da dama suka jikkata.
A cewar sanarwar, Madam Zuma ta kara bayyana damuwa kan yadda ake yawaita kai hare-hare a yankin arewacin Mali da sauran kasashen da ke shiyyar.
Sai dai Uwar gida Zuma ta bayyana kudurin kungiyar AU na nuna goyon baya ga Mali da tawagar MINUSMA, musamman gwamnatin Togo da mutanen da wannan lamarin ya shafa.
Ta kuma yi amfani da wannan dama wajen mika sakon ta'aziyar kungiyar ta AU ga iyalan wadanda suka rasa 'yan uwansu,tare da fatan samun sauki cikin hanzari ga wadanda suka jikkata.
Madam Zuma ta kuma yaba rawar da dakarun ke takawa a yankin.(Ibrahim)