in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin da aka kai wa motocin sojan kasar Mali ya haddasa mutuwar wasu 5
2016-05-28 12:35:58 cri
Wasu motocin rundunar sojan kasar Mali guda 2 sun gamu da harin boma-bomai a arewacin kasar a jiya Jumma'a, lamarin da ya haddasa mutuwar wasu sojoji 5, gami da raunatar wasu 4.

Wata sanarwar da ma'aikatar tsaron kasar Mali ta gabatar a jiya Jumma'a 27 ga wata, ta ce, wadannan motoci guda 2 suna wajen kan iyakar yankin Gao da yankin Menaka ne duk a arewacin kasar Mali, lokacin da suka gamu da harin fashewar wata nakiya. Dukkan mutanen da suka rasa rayuka da jin raunuka sakamakon harin nan sojoji ne dake cikin motocin 2.

A cikin sanarwar, ma'aikatar tsaron kasar Mali ta ce gwamnatin kasar za ta yi iyakacin kokarinta don gurfanar da wadanda suka kai wannan harin gaban kotu.

Sai dai har zuwa yanzu, babu wata kungiya ko wani mutum da ya yi ikirarin daukar alhakin wannan hari. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China