Jiya rana ce ta ma'aikatan kiyaye zaman lafiya ta duniya. A wannan rana, ta bakin kakakinsa, Ban Ki-moon ya ba da sanarwar cewa, an aikata wannan danyen aiki a wannan ranar da kamata a girmama jaruntaka da sadaukar da rai da ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na MDD suka nuna, lallai wannan abin bakin ciki ne kwarai.
Bisa dokokin kasa da kasa, irin wannan harin da aka kaddamar tamkar laifin yaki ne. Don haka ya yi kira da a hanzarta cafke wadanda suka kai wannan harin.
Bugu da kari, a wannan rana, kwamitin sulhun MDD ya ba da wata sanarwar yin allah-wadai da babbar murya kan wannan hari, kana ya kalubalanci gwamnatin Mali da ta hanzarta gudanar da bincike kan harin.(Fatima)