in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takaitattun labarai daga wasu Jaridun Najeriya(160531)
2016-05-31 19:25:40 cri

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya ce bai taba tsammanin tsohon shugaban kasar da ya gada wato Goodluck Jonathan zai amince da shan kaye ba, biyowa bayan babban zaben kasar na bara. (The Punch)

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tura wasu manyan jirenga ruwan yaki guda 5, da jiragen ruwa masu dauke da bindigogi, da wasu karin kananan jiragen yaki na sama, zuwa yankin Niger Delta mai arzikin mai, a wani mataki na dakile ayyukan tsagerun yankin dake lalata kayayyakin kamfanonin hakar mai. (Vanguard)

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya yi kira ga 'yan majalissar dokokin kasar, da su hanzarta zartas da dokar yaki da safarar haramtattun kudade ta shekarar 2016, tare da sauran dokokin dake gaban zauren majalissun kasar. Shugaban ya yi wannan kira ne a daren jiya, yayin liyafar da 'yan majalissun kasar suka halarta a fadar gwamnati dake birnin Abuja.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China