in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya na fatan fadada hadin gwiwar tattalin arziki da wasu kasashen Afirka takwas
2016-05-26 09:51:35 cri
Ministan harkokin wajen tarayyar Najeriya Geoffrey Onyeama, ya ce kasarsa na fatan bunkasa hadin gwiwar tattalin arziki da wasu kasashen Afirka takwas, karkashin wasu yarjeniyoyi da za su kulla nan gaba kadan da kasashen.

Mr. Onyeama ya ce yarjejeniyoyin za su shafi baiwa al'ummun kasashen damar shiga kasashen juna ba tare da visa ba. Hakan a cewarsa zai bude kofofin kasuwanci da cinikayya, tare da kawar da shingen dake dakile cimma moriyar juna tsakanin sassan nahiyar Afirka.

Har wa yau, ministan ya tabbatar da cewa cikin shekara guda za a gama dukkanin shirye-shirye, wadanda za su ba da damar aiwatar da wannan manufa. Kana daga bisani ana fatan sauran kasashen nahiyar su ma za su yi koyi da wannan hikima.

Mr. Onyeama ya kara da cewa daukar matakai makamantan wadannan yana da sauki, fiye da bi ta karkashin kungiyoyin shiyya shiyya kamar ECOWAS da sai sauran su, duba da tsawon lokaci da ake kwashewa kafin cimma matsaya karkashin wadannan kungiyoyi. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China