in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takaitattun labarai daga jaridun Najeriya
2016-05-25 18:53:36 cri
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya bayyana cewa, gwamnatin tarayyar kasar tana shirin bullo da wasu matakai da nufin magance yawan hare-haren da 'yan tawaye ke kaiwa bututun mai a yankin Niger Delta(Daliy Trust)

Kwamitin kula da manufofin kudi na babban bankin Najeriya ya umarci hukumar gudanarwar bankin da ta bullo da wani tsarin musayar kudi mai sassauci tsakanin bankunan kasar.

Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefele ne ya bayyana hakan jiya Talata, lokacin da ya ke jawabi ga manema labarai jim kadan bayan kammala taron yini biyu da kwamitin manufofin kudi na bankin MPC ya gudanar a hedkwatar babban bankin da ke Abuja, fadar mulkin Najeriya.(The Punch)

A yau Laraba ne gwamnatin tarayyar Najeriya, za ta koma teburin sulhu da kungiyar kwadagon kasar bangaren Ayuba Wabba, sakamako janye yajin aikin kasa baki daya da suka shirya gudanarwa, domin tilastawa gwamnati janye karin farashin man fetur din da ta yi.(Vanguard)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China