A cikin wata sanarwa, kamfanin, dake aiki tare da kamfanin man fetur na Agip na Najeriya (NAOC), ya bayyana cewa harin na ranar Lahadi kan bututunsa dake jihar Bayelsa ya rage samar da man fetur dinsa na gangunan mai 4200 a kowace rana.
Wannan na sa kamfanonin sun kasa cika alkawuransu na aiki dalilin abubuwan da suka wuce ikonsu.
A farkon watan Mayu, Kamfanonin Shell da Exxon Mobil sun bayyana matsalar da ta fi karfinsu a yankin Niger Delta, inda masu fafatuka suka fara kai hare-hare da janyo wani ja da baya ga fitar da man fetur daga Najeriya.
A ranar Laraban da ta gabata, wani harin ya janyo asarar kimanin gangunan mai 1000, tare da haddasa wata asarar ajimilce ta samar da gangunan mai 5200 a bangaren kamfanin hakar mai na Eni.
A ranar, gwamnatin Najeriya ta sanar da daura damarar yaki da kungiyar Niger Delta Avengers (NDA), wani sabon gungun masu fafutuka dake yankin, domin kawo karshen hare hare kan gine ginen man fetur da gas. (Maman Ada)