in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takaitattun labarai daga jaridun Najeriya
2016-05-27 19:23:08 cri
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta gana da wasu wakilan 'yan tawaye daga yankin Niger Delta, sakamakon hare-haren da 'yan tawayen yankin ke ci gaba da kaiwa bututan mai da ke yankin.(The punch)

Ministan watsa labarai da al'adun na Najeriya Lai Mohammed ya sake nanata kudurin gwamnatin kasar na gaggauta farfado da tattalin arzikin kasar.

Ministan wanda ya bayyana hakan ne jiya Alhamis yayin da ya ke ganawa da wasu ministoci da mambobin hukumar watsa labaran kasar(BON) a Abuja,fadar mulkin kasar, ya kuma ba da tabbacin cewa, sama da 'yan Najeriya miliyan 8 za su amfana kai tsaye da shirin gwamnati na tallafawa matasa, baya ga wasu miliyoyi da su ma za su ci gajiyar wannan asusu ta wata fuska.(Daily Trust)

A jiya ne kuma gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce shirin da ta ke yi na dawo da jiragen sama na kasar zai karfafa takara a bangaren zirga-zirgar jiragen saman kasar. Karamin Ministan zirga-zirgar jiragen sama na kasar Hadi Sirika ne ya bayyana hakan a Abuja, lokacin da ya tarbi shugabannin kungiyar manyan ma'aikatan sufuri ta Najeriya(ATSSSAN) karkashin jagorancin shugaban kungiyar Benjamin Okewu.(Vanguard)

Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Laftana janar Tukur Buratai ya tabbatar da cewa, watakila Fulani makiyaya da ake zargin da kai hare-hare kan wasu al'ummomin kasar,suna da alaka da 'yan ta'adan Boko Haram.(The Guardian)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China