in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takaitattun labarai daga jaridun Najeriya
2016-05-26 19:03:22 cri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce tattalin arzikin kasar yana cikin wani hali na ha'ula'i sakamakon faduwar farshin mai a kasuwannin duniya.

Shugaban ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da farashin man ya tashi da kusan dala 50 kan kowa ce ganga. Koda ya ke Najeriya ba za ta amfana sosai da tashin farashin man ba, sakamakon raguwar yawan man da ta ke hakowa a 'yan kwanakin nan.(Daliy Trust)

A jiya Labara ne majalisar dattawan Najeriya ta gayyaci ministar kudin kasar Kemi Adeosun da gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefele domin su yi mata bayani game da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, lamarin da ya haifar da karuwar farashin kayayaki,rashin aikin yi, talauci da faduwar kudaden shiga da kasar ke samu a bangaren mai da sauran matsaloli, da kuma matakan da aka dauka don ceto tattalin arzikin kasar daga halin da ya tsinci kansa a ciki.(The Guardian)

A daya hannun kuma kwamitin majalisar wakilan Najeriya mai kula da sayar da kadarorin gwamnati ya dakatar da wani shiri na kamfanin man fetur na kasar game da sayar da matatun man kasar guda uku wato matatun man fatakwal,Kaduna da kuma Warri.(Vanguard)

Gwamnatin tarayyar Najeriya da babbar kungiyar kwadagon kasar(NLC) sun kafa wani kwamiti mai wakilai 16 da zai tsara matakan da zai kai ga bullo da sabon tsarin albashin ma'aikata da nufin magance tasirin karin farashin man fetur da aka yi a kasar.(The Punch)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China