Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya karyata rahotanni da wasu jaridun kasar ke yayatawa a jiya cewa, yana shirin neman mafakar siyasa a daya daga cikin kasashen da ke yammacin Afirka, sakamakon rahoton da ke cewa, hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa tana shirin bincikar gwamnatinsa da ta gabata bisa zargin aikata cin hanci da rashawa.
Sai dai kakakinsa Reno Omokri, ya ce tsohon shugaban kasar ya ba shi tabbacin cewa, zai dawo Najeriya da zarar ya kammala ziyararsa a birane daban daban.(The Guardian)
Mai magana da yawun rundunar sojojin Najeriya kanar Sani Usman ya ce, daya daga cikin manyan masu harhadawa kungiyar Boko Haram bama-bamai ya gamu da ajalinsa, sakamakon yadda wani dan kungiyar ya harbe shi a lokacin da yake kokarin tserewa daga cikin kungiyar a jiya Litinin.
Kanar Sani ya bayyana lamarin a matsayin wani muhimmin ci gaba a yakin da dakarun kasar ta Najeriya suke yi na kakkabe 'yan ta'addan.(Daliy Trust)