Cikin bayanin da ya yi, Mr. Ouyang ya ce, anihin batun Tekun Kudu shi ne batun mallakar wasu kanannan tsibirai a yankin kasar Sin da kasar Philippines ta yi ba bisa doka ba, da kuma wasu matsalolin dake shafar yanke iyakar teku bisa kafuwar sabuwar tsarin dokar teku.
Sa'an nan, Mr. Ouyang ya kara da cewa, yarjejeniyar dokar teku ta MDD ba ta shafi ikon mallakar yankin teku ba, shi ya sa, kasar Sin ta riga ta sanar da cewa, ba ta amince da wannan yarjejeniya a kan batun yanke iyakar teku ba, shi ya sa, kasar Sin ta ba da sanarwar cewar ba ta amince da kuma halartar hukuncin da za a yanke kan karar Tekun Kudu da kasar Philippines ta gabatar ba, wannan matakin da kasar Sin ta dauka ya dace da yarjejeniyar da sauran dokokin kasa da kasa. Sabo da an yanke wannan hukunci ba bisa doka ba, shi ya sa, kasar Sin ba za ta amince da kuma karbar sakamakon da za a fidda game da wannan kara ba. (Maryam)