Kayayyakin agajin sun hada da tantuna da barguna wadanda wani jirgin saman daukar kaya na kamfanin jiragen saman kudancin kasar Sin ya yi jigilarsu, an mika su ga ma'aikatar kula da walwala da ci-gaban al'umma ta kasar Philippines, daga bisani kuma za'a kai su garin Tacloban dake tsakiyar yankin Leyte, inda nan ne guguwar ta fi yi ma mummunar barna.
Mercedita Jabagat, darekta yankin Philippine na ofishi na 7 ya ce, tantunan da barguna ana da matukar bukatar su, musamman wadanda suka tsira da ransu a wannan bala'in guguwa, wanda daga nan sai ya mika godiyar daukacin al'ummar kasar bisa ga wannan gudummuwar da kasar Sin ta bayar.
Wu Zhengping, kansila a sashen tattalin arziki da ciniki na ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Philippines ya bayyana cewa, guguwar ta Haiyan ta kawo babbar asara ga kasar Philippines, abin da ya janyo damuwa kwarai daga sauran kasashen duniya, kasar Sin tana nuna matukar tausayawarta da kuma kulawarta sannan a shirye take ta taimakama wadanda wannan bala'i ya shafa, don haka ya tabbatar da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da ba da taimakonta a ko wane fanni game da hakan.
Kasar Sin ta ba da gudumuwa ta kayayyakin agaji da darajarsu ta kai adadin kudin RMB miliyan goma kwatankwacin kudin Philippines Pesos miliyan 73.2 domin agaza ma wadanda wannan bala'i ya shafa, ban da tsabar kudi na dalar Amurka miliyan 200 da gwamnatin kasar tare da kungiyar ba da agaji ta Red Cross suka bayar tare.(Fatimah)