A yau Litinin ne Lu Kang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya musunta kalaman da ke cewar, wai saboda babban bambancin karfi da ke tsakanin kasashen Sin da Philippines ne ya tilastawa Philippines ta gabatar da kara a gaban kotu dangane da tekun kudancin kasar Sin. Lu ya yi nuni da cewa, wadannan kalamai an yi su ne kawai domin a shafa wa kasar Sin kashin kaji.
Lu Kang ya fadi haka ne a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, inda ya kara da cewa, kasar Sin ba za ta ci zarafin kowace kasa ba, amma ba za ta yarda wasu su yi mata sharri ta hanyar da ba ta dace ba. (Tasallah Yuan)