Yayin taron manema labaran da aka yi a ranar 27 ga wata, Qin Gang ya bayyana cewa, ma'aikatan samar da agaji da kasar Sin ta tura zuwa kasar Philippines dake kunshe da masu samar da agajin gaggawa, likitoci da kuma jirgin ruwan bada jinya sun dukufa wajen gudanar da ayyukansu tun isarsu kasar Philippines, inda suka ceto mutane sama da dubu daya, da kuma gano gawawwaki guda 22. Mr. Qin ya bayyana cewa, ma'aikatan za su ci gaba da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, kuma gwamnatin kasar Philippines ta bayyana matukar godiya bisa ga taimakon da ma'aikatan kasar Sin suka bayar a wannan kasa. (Maryam)