in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bukaci Philippines da ta koma kan teburin sulhu game da batun tekun kudancin kasar Sin
2015-12-21 19:43:54 cri
Kasar Sin ta bukaci kasar Philippines da ta dawo kan teburin tattauna dangane da takaddamar da ke tsakaninsu game da batun tekun kudancin kasar ta Sin.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Hong Lei wanda ya bayyana hakan a yau yayin taron manema labarai a nan birnin Beijing, ya kuma nanata cewa, kasar Sin ba za ta taba amincewa da shiga kotu da kasar Philippines game da batun tekun kudancin kasar Sin ba.

Mr. Hong ya ce, Sinawa ne ke da ikon yanke shawara game da 'yancin kasar Sin amma ba wasu mutane ko kungiya ba.

Mr. Hong ya ce, kasar Sin ba za ta amince da duk wani sakamako da wani bangare can zai bayar game da wannan takaddama ba. Don haka ta bukaci kasar Philippines da ta canja matsayinta kana ta dawo kan teburin tattaunawa.

Kasar Sin dai ta ki yarda ta shiga zaman kotun, tana mai cewa kamata ya yi kasashen da batun ya shafa kai tsaye su warware matsalarsu ta hanyar tuntubar juna da tattaunawa.

A farkon shekarar 2013 ne kasar Philippines ta shigar da kara game da wannan batu a gaban wata kotun kasa da kasa da ke birnin Hague.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China