A gun taron manema labaru da aka saba yi a wannan rana, Hong Lei ya bayyana cewa, a ranar 10 ga wata, bayan da jirgin ruwa dauke da asibitin da ke kula da marasa lafiya na tafi-da-gidanka mai suna ARK Peace ya kammala ba da aikin jin kai a wuraren da ke fama da bala'in mahaukaciyar guguwar da ta abkawa kasar Philippines, ya koma kasar Sin daga tashar ruwa dake yankin Gulf na Leyte na Philippines. Wannan shi ne karo na farko da kasar Sin ta tura jiragen ruwa don ba da aikin jinya a kasashen da bala'in ya shafa. A cikin kwanaki 16, jirgin ruwa dauke da asibitin tafi-da-gidanka na ARK Peace ya yi aikin jinya ga mutanen da suka ji rauni 2208, kuma an yiwa mutane 44 tiyata . Ban da wannan kuma, an duba lafiyar jikin jama'a, tare da binciken annoba, da aikin duba ingancin ruwa a wuraren da bala'in ya shafa da sauransu, kana kuma, ya ba da kyautar kayayyakin kiwon lafiya ga kasar Philippines.(Bako)