Ranar 29 ga watan Mayu rana ce ta ma'aikatan kiyaye tsaron kasa da kasa na MDD, a halin yanzu, gaba daya MDD ta tura tawagogin kiyaye tsaro na musammun guda 16 zuwa wasu kasashen duniya, haka kuma, kimanin ma'aikatan kiyaye tsaro dubu 124 sun shiga wadannan ayyukan kiyaye tsaro.
Kaza lika, tun lokacin da kasar Sin ta fara shiga wannan aiki na kiyaye tsaron kasa da kasa a shekarar 1990, ya zuwa yanzu, gaba daya kasar ta aike da ma'aikata sama da dubu 30 domin halartar wannan aiki, lamarin da ya sa, kasar Sin ta kasance zaunanniyar mambar kwamitin sulhu na MDD da ta fi aike da ma'aikatan kiyaye tsaro ga kasa da kasa, inda ta kuma cimma alkawarinta sosai wajen kiyaye zaman lafiyar kasa da kasa, yayin da take daukar alhakinta yadda ya kamata a wannan fanni cikin gamayyar kasa da kasa. (Maryam)