Kakakin rundunar sojin kasar Sani Usman ya tabbatar da cewar sojojin kasar sun ceto mutanen ne a lokacin wani simame a shiyyar arewa maso gabashin kasar tsakanin ranar 26 ga watan Fabrairu zuwa 31 ga watan Maris.
Ya ce yawancinsu, an same su ne a wasu kauyuka da garuruwa da mayakan Boko Haram suka boye su, sannan an karbo wasu daga hukumomin jamhuriya Kamaru.
Usman ya ce, dakarun kasar zasu ci gaba da gudanar da sintiri domin maido da zaman lafiya a shiyyar arewa maso gabashin kasar.
Hare haren Boko Haram ya yi sanadiyyar hallakar dubban jama'a, mafi yawa a shiyyar arewa maso gabashin kasar, tun bayan da suka kaddamar da yaki a shekarar 2009, a yunkurin kafa daular musulunci.
Sai dai dakarun Najeriya sun yi nasarar kwace mafi yawan yankunan dake karkashin ikon mayakan Boko Haram, amma har yanzu kungiya tana iya kaddamar da hare hare a wasu daga cikin yankunan kasar.(Ahmad Fagam)