Shugaban kasar Sin: kamata ya yi a yi kokari don tabbatar da tsaron kasa
A gabannin ranar 15 ga wata, wato ranar fadakar da jama'a game da tsaron kasa ta farko ta kasar Sin, shugaba Xi Jinping na kasar ya ba da umurni mai muhimmanci, inda ya jaddada cewa, tabbatar da tsaron kasa babban buri ne na jama'a, shi ne kuma babban aiki da ya fi kome muhimmanci ta fuskar cimma burin kasar Sin na farfadowar al'ummar kasar, da ba da tabbaci ga jama'a ta yadda za su gudanar da ayyukansu da yin zama yadda ya kamata. (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku