in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana da Amurka sun rattaba hannu kan hadin gwiwwar tsaro
2016-02-20 12:57:16 cri

Kasar Ghana da Amurka sun rattaba hannu a kan hadin gwiwwar tsaro da zai sa kasar dake yammacin Afrika ta inganta yanayin tsaron ta da rashin daidaito.

Yarjejeniyar mai taken SGI na hadin gwiwwa da kasashen yana da nufin hadin gwiwwa ne da hada bayanai a kan nazarin damammaki da kalubaloli da gwamnati ke fuskanta.

Manufofin da burin shirin shi ne kara karfin kasashen da ake hadin gwiwwar da su wajen biyan bukatun al'umma a bangaren tsaro, kare tare da hana zaman fargaba da ake ciki da kuma tashin hakali, sannan a dakile hare-haren 'yan ta'adda da wuraren da suka yi kaka gida. A inganta mulkin demokuradiya, bin doka, da mutunta 'yancin dan adam da dai sauran su.

Yarjejeniyar har ila yau za ta hada Ghana da wassu kasashe 5 na Afrika aiki tare domin inganta bangaren tsaron su da kuma karfin su wajen fuskantar kalubale da suka hada da kungiyoyin 'yan ta'adda, miyagun ayyuka, laifuka ta yanar gizo, bada tsaro a kan teku da kiyaye fashin tekun.

A karkashin shirin, Amurka za ta taimaki wadannan kasashe wajen inganta dabarun tsaron su ta hanyar rarraba bayanai a tsakanin su.

Ministar harkokin wajen kasar Ghana Hanna Serwaa Tetteh ta ce, shirin zai taimaka ma kasar da sauran kasashen Afrikan da aka zaba karfafa hukumominsu tinkarar duk wassu barazanar tsaro da ke nan ko yake shirin bullowa a nahiyar.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China