Wata tawagar dakarun wanzar da zaman lafiya mai kunshe da jami'ai 195, ta tashi daga kasar Sin zuwa kasar Mali a jiya Laraba, domin fara ayyukan wanzar da zaman kafiya karkashin tawagar MDD.
Wannan tawaga dai ita ce ta 4 da Sin ta tura. Bayan isar ragowar 'yan tawagar a ranar 26 ga wata, jimillar jami'an na Sin za su kai 395, wadanda kuma da isar su za ta maye gurbin tawaga ta uku.
Tawagar dai ta hada da injiniyoyi, da dakarun tsaro da kuma jami'an lafiya, za kuma su kasance a kasar ta Mali tsawon shekara guda.